Dan wasan Real Madrid Ronaldo zai kara samun yaro kwanan nan
- Ba mamaki kwanan nan Budurwar babban Dan wasan ta sauka
- Tun kwanakin baya Cristiano Ronaldo ya tabbatar da juna biyun
Mun fahimci cewa gwarzon Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo zai kara samun yaro kwanan nan.
Babban Dan wasan gaban Duniya Ronaldo na daf da zama uba karo na 4 a Duniya da zarar Budurwar sa Georgina Rodriguez ta sauka. Wannan ne dai karo na farko da wata Budurwar Dan wasan za ta haihu bayan ya samu 'ya 'ya 3 wanda har yau ba a san Mahaifan su ba.
KU KARANTA: Ronaldo ba sa'a na bane- Inji Pele
Hoto daga GoffPhotos
Tun a watan Yuli Dan wasan ya tabbatar da cewa Budurwar ta sa na da juna biyu kuma ba mamaki yanzu ta kusa sauka. Yanzu dai akalla an dauki kusan shekara guda kenan Ronaldo yana tare da Rodriguez wanda ta ke aiki a Kamfanin Gucci.
Babban Dan wasan yana da 'ya 'ya 3 yanzu wanda babban yake da shekaru 7 sannan kuma ya samu tagwaye kwanan nan. Dan wasan yace yadda yake goya lamba 7 haka yake so ya goya 'ya 'ya 7.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a
Adaadakawa@gmail.com
No comments
Post a Comment