Pages

Games

Tuesday, 2 January 2018

Malaman Addini Na Samun Salon Wa’azin Su Ne Daga Fina-finan Mu – Rashida Lobbo

Wata sabuwar jarumar Kannywood da wasu masu fashin baki ke cewa ta shigo masana’antar da kafar dama tayi ikirarin cewa malaman addini suna samun salon yadda za su yi wa’azin su ne daga fina – finan hausa.Rashida Lobbo dai tana daya daga cikin jaruman da suka karbi kyauta a bikin karama jaruman fim da mujalar city people ta shirya kwanakin baya a jihar Lagos.
Rashida Lobbo wacce ake wa lakabi da yar Yola tana cikin sabbin jarumai da tauraronsu ke haskawa kuma da alama ta shirya damawa da sauran fitattun jarumai dake masana’antar cikin shekarar 2018 da zamu shiga.
Kamar yadda ta bayyana a shafin ta na sada zumunta na facebook, jarumar tana karkashin kamfanin shirya fina-fina na FKD wato mallakar shahararen jarumi, Ali Nuhu

No comments

Post a Comment

Designed With & By Abijah Johnnie
Designed With & By Abijah Johnnie